Magance Matsalolin Tsaro: Chadi za ta Kara Yawan Sojojinta Zuwa 60,000

 

Gwamnatin sojojin Chadi ta ce tana shirin kara yawan dakarun kasar domin magance matsalolin tsaro da suka hada da barazanar ‘yan ta’adda da kuma ‘yan tawaye.

Ministan tsaron kasar Janar Daoud Yaya Brahim ya shaida wa majalisa cewa rundunar sojin Chadi ta fara shirin kara yawan sojojin daga 35,000 zuwa 60,000 a shekarar 2022.

Ya ce tuni har sun fara daukar mutane tare da ba da horo, kuma manufar a cewarsa ita ce samar da rundunar da za ta magance kalubalen da ke fuskantar yankin Sahel.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here