Gwamnatin Kigali ta Tallafawa Mata 120 da Baburan Zamani da ke Amfani da Lantarki

An kaddamar da shirin tallafawa mata da rage fitar da hayaƙi mai gurbata muhalli a birnin Kigali na Rwanda ta hanyar soma tallafawa mata 120 da baburan zamani da ke amfani da lantarki.

Matan sun samu horo na wata uku kan tukin babur da kuma yada ake sarafa babur din na zamani, kuma a yanzu sun shirya domin samu aiki, da kuma kare muhalli.

Maza ne dai suka mamaye harkar kasuwancin sufuri a biranen Rwanda, sai dai Ornella Owobasa da ta bai wa matan horo na cewa suna son ganin sauyi kan hakan.

Ɗaya daga cikin matan da suka samu horo, Jasmine Niyigaba, ta ce a shirye take to soma wannan sana’a da karaɗe tittuna a Rwanda.

Mataimakin magajin birnin Kigali, Martine Urujeni, ya ce shirin zai taimakawa wajen rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli da rage gibin rashin ayyukanyi tsakanin matasa da mata.

Kusan mutane dubu 35 ke da rajista a Kigali don achaba, sai dai galibinsu maza ne, abin da ya sa mahukunta a wannan lokaci ke cewa za a ga sauyi.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here