Rijistar Jam’iyyar APC: Muhammad Rili Yayi Kira Ga Matasa Da Su Shiga Siyasa Domin A Dama Dasu

 

A shirye shiryen da Jam’iyya mai rike da mulki ta All Progressive Congress (APC) ke yi na fara yin rijista ga al’umma da sabuntawa, wanda za a fara gudanarwa a 2nd Fabrairun 2021.

Mallam Muhammad Rili yayi kira ga al’ummar Nijeriya,musamman matasa da suyi wannan rijista domin samun cikakkiyar damar da za a dama dasu a siyasance tun daga tushe.

Idan za a tuna Gwamnati mai ci a yanzu ta APC ta fitar da allon jadawalin tsarin yin rajista ga membobi da masu sha’awar shiga jam’iyyar Wanda za a fara a 2nd Fabrairu 2021, a dukkanin jahohi 36 na kasar nan dama birnin tarayyar Abuja.

Malam Muhammad Rili ya bayyana cewar a kowane tsarin siyasa mai ‘yanci indai ana bukatar nagartaccen cigaba mai dorewa, to yazama wajibi mutane su suka hannun su a cikin fatan da suke na samun cigaba.

A karshe Mallam Muhammad Rili ya yayi kira tattausa ga ‘yan Najeriya da suka cigaba da zama masu kishin kasa da son al’umma a kowane yanayi da mataki.

Malam Muhammad Rili matashin dan siyasa ne mai kishin ganin sauyi mai amfani, da dabbaka zaman lafiya a cikin siyasa da al’ummar Najeriya baki daya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here