An yi Kira ga Shugaba Tinubu da ya Tsige Ribadu a Matsayin Mai Bada Shawara Kan Tsaro

 

An fara kira ga shugaban kasa Bola Tinubu kan ya tsige Nuhu Ribadu a matsayin mai bada shawara kan tsaro saboda furucinsa na baya-bayan nan.

A wajen wani taro, tsohon shugaban na EFCC ya fito fili ya caccaki gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta gaji tsiya daga gwamnatin baya, cewa shine dalilin matsin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.

FCT, Abuja – An shawarci Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya tsige babban mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro kuma tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Nuhu Ribadu.

Wannan kira na kunshe ne a cikin wani rubutun ra’ayi da wani marubuci mazaunin Abuja, Abbah Modibo ya yi a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda yake kunshe a rubutun wanda Legit ta samu, Modibo ya bayyana cewa Ribadu bai cancanci rike wannan muhimmin mukami kamar da mai ba kasa shawara kan tsaro ba.

Ya bayyana dalilinsa kan furucin da Ribadu ya yi cewa gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tsiyata kasar kafin ta mika mulki ga Shugaba Tinubu.

A wani rahoto da Legit Hausa ta fitar a baya, an nakalto Ribadu yana cewa:

“Muna fuskantar cikas sosai wajen kasafin kudi. Zai yi kyau in fada maku. Zai yi kyau ku sani. Mu na cikin halin ha’ula’i.

“Mun gaji kasa mai wahalar sha’ani, kasa a tsiyace har ta kai mu na biyan bashin abin da aka dauka. Abin ya yi kamari.

“Amma gwamnatin nan ta na yin bakin kokarinta wajen ganin mun sauke nauyin da ya rataya, daga ciki har da na sojoji.”

Dalilin da yasa ya zama dole Tinubu ya kori Ribadu – Madibbo

Da yake martani kan furucin Ribadu, Madibbo ya ce:

“Idan har akwai wata hujja da ke nuna rashin sani da jahilcin Nuhu Ribadu, zarge-zargen da ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kwanan nan ya tabbatar da hakan.

“A takaice Nuhu Ribadu bai dace da zama mutumin da zai riki ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ba, kuma ya kamata a gaggauta sauke shi kafin ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.”

Modibbo ya kuma bayyana cewa furucin Ribadu ya bai wa jam’iyyun adawa makamin da suke bukata don farfadowa daga rikcin cikin gida da suka fada.

Ya ce jawabin ya kuma ruguza karin kokarin da shugaban jam’iyyar APC ke yi na gyara jam’iyyar.

Ya bukaci Shugaba Tinubu da ya yi wa tufkar hanci sannan ya gaggauta korar Ribadu a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com