Yadda Kiran Salla ya yi Tasiri a Rayuwata – Jaruma Tonto Dikeh

 

Jarumar fim a masana’antar Nollywood, Tonto Dikeh ta yi magana kan yadda kiran salla ya yi tasiri a rayuwarta.

Dikeh ta ce sautin kiran salla ya sauya mata rayuwa inda ya kara kusanta ta da addini inda ta ce Musulmai suna burgeta.

Jarumar wacce Kirista ce ta ce tana neman shawara yadda za ta ba masallacin tallafi amma ba ta hanyar kudi ba.

Jihar Lagos – Jarumar fina-finan Nollywood, Tonto Dikeh ta yi magana kan yadda Musulmai ke burge ta.

Jarumar wacce Kirista ce ta ce yadda Musulmai ke rike addininsu hannu bibbiyu yana matukar burgeta.

Jaruma Tonto Dikeh ta magantu kan Musulunci

Tonto Dikeh ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram inda ta ce tana jin dadin yadda ake kiran sallah.

Jarumar ta ce tana rayuwa kusa da masallaci wanda haka ya saka ta fara sha’awar musulunci inda ta ce kullum tana tashi saboda kiran salla da ake yi.

Ta ce karar sautin kiran sallah yana kara kusanta ta ga Allah da kuma dagewa wurin yin addini.

Tonto Dikeh ta nemi shawara ƴan uwa

“Allah/Ubangiji abin so ne, gaskiya na sha jinin jikina, addu’ar da nake yi shi ne yadda zan fahimci Musulunci sosai.”

“Yadda suke dagewa a wurin addininsu abin koyi ne, ina ji a jiki na kamar na je masallacin na tambaya me yasa basu yi sallah ba yau.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here