Shugabannin Addinin Kirista Sun Kai wa Sheikh El-Zakzaky Ziyara

Wasu shugabannin addinin Kirista sun kai wa shugaban kungiyar ƴan Shi’a a Najeriya ta Harakar Islamiyya, IMN, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ziyarar goyon baya, sakamakon sakinsa da babbar kotun jahar Kaduna ta yi bayan tsare shi da matarsa Zeenat da aka yi kusan shekara shida.

Ƴan tawagar ta fasto-fasto da suka ziyarci jagoran na IMN wata biyu bayan da kotun ta sake shi, sun ce ƙari a kan goyon bayan sun kuma je ne domin su nuna godiya kan taimakon abincin da yake bai wa matan Kiristoci da suka rasa mazajensu a sanadiyyar matsalar rashin tsaro, kamar yadda sanarwar da mataimakin sashen yada labarai na kungiyar ta IMN Abdullahi Usman ya fitar ta nuna.

A sanarwar wadda jaridar Punch ta Najeriya ta wallafa, El-Zakzaky wanda ya bayyana irin mawuyacin halin da ya shiga da matarsa, ya ce kusan shekara shida bayan harin watan Disamba na 2015 da sojoji suka kai masa da magoya bayansa har yanzu akwai ɓurɓushin harsashi a jikinsa da na matarsa Zeenat.

Ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da aikin jin ƙai, yana mai cewa bayar da taimakon abinci abu ne da ya wajaba domin yaƙi da yunwa a Najeriya.

Da yake bayyana malaman Kiristan da suka ziyarce shi a matsayin ‘yan uwa wajen kyautata wa al’umma, malamin ya ce in ba domin yanayin lafiyarsa ba da rashin tsaro a kasar da zai so ya hadu da ƙarin mutane.

Daga cikin ƴan tawagar Kiristocin akwai Fasto Yohanna Buru daga Kaduna da Rabaran Titus Ishaku daga Cocin Baptist ta Jos da Rabaran John Ahmadu daga Abuja da Rabaran Peter Audu shi ma daga Abuja sai Rabaran George T. John na Kaduna tare da Fasto Julius Audu.

Rabaran John Ahmadu ya ce kafin haɗuwa da El-Zakzaky, yadda yake ɗaukar Musulmi da Musulunci da ban ne.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here