Jam’iyar PDP ita ce jam’iyar adawa mafi girma tun kirkirar jahar Zamfara a 1996 da Fara dimokaradiya a 1999. Duk da cewa jam’iyar ta Jagoranci Najeriya har Shekaru 16. Haka zalika duk da cewa jam’iyar ta yi nasarar karbar Gwamna Dungurugum! Daga 2008/2011 Amma Hakan bai sa jam’iyar ta yi nasara kafa Tarihin cin Zaben jahar ba a 2011 duk da cewa Gwamnan da ke ci ne a lokacin ne ya yiwa jam’iyar takarar Gwamna. Inda ya sha Kaye hannun Gwamna Mai ci a yanzu.

Duk da dai cewa, Muna ta’allaka rashin cin zaben PDP da rashin karbuwar jam’iyar ga talakawan jahar, da kuma yadda Talakan jahar suka rungumi jam’iyar APP, ANPP har zuwa yanzu da ta yi maja zuwa APC.

Sai dai saboda wasu dalillai dai da na ke iya Kiransu son rai na tsiraru, ya sa jam’iyar na shirin rasa ‘yan takarkari baki daya na jahar Zamfara. Hakan na nufin kenan dama ta samu ga jam’iyar adawa ta PDP (Ganin ita ce mafi girma a jahar). Sai dai! Abunda zan iya Kira da rashin kishi da manufa, ya sa jam’iyar kusan gwamma jiya da yau. Idan mu ka dubi Shekarun da suka wuce, irin tasirin PDP da yanzu, to ba abunda za mu ce, sai dai ko WA ya tuna bara.

La’akkari da kusan halin suman da jam’iyar take a halin yanzu. Yayin da ya rage saura kwanaki 72 a shiga zaben 2019. Amma har yanzu ba wani hubbasa da jam’iyar ta ke yi a jahar Zamfara.

HUJJA!

Tun da jam’iyar ta fadi Zabe kamar yadda ta Saba a 2015. Kwata-kwata jiga-jiganta suka kwashe inasu-inasu suka bar jahar, Wanda wasunsu har yanzu ba su dawo jahar ba. Wanda ko adawar da ake hasashen jam’iyar ta yi, ba wani alamar akwaita a jahar balantana a ga ta yi adawar Dan kawo sauyi. Duk wani Abu da yafi jam’iyar PDP to ba Maganar taka rawar gani wannan ya sa da dama daga cikin ‘ya’yanta guiwarsu ta yi Sanyi. Wasu suka Barta, wasu kuma suna cikinta rai kwakwai-mutu-kwakwai….

Ba ni mantawa tsakkiyar wannan shekarar mun zo wani gangami da wani kudurin da mu ke so ya zama doka (nottooyoungtorun) kiri-kiri duk da mun kaiwa jam’iyar shedar cewa za mu zo Amma muka tarar da SHELKWATAR jam’iyar da ke Gusau a garkame, abunda ya sa dole mu ka yi gaba zuwa wajen takwarorinta.

Na yi mamaki matukar gaske yau da na ga wata Kungiya Mai suna AdvocacyNigeria ta shirya MUHAWARA ga ‘yan takarar Gwamna 5 na jahar Zamfara. Wanda jam’iyar PDP na cikinsu. Amma abun mamaki dukkan jam’iyun sun halarci MUHAWARAR Hasalima jam’iya daya ce Dan takarar MataimaKin gwamna ya wakilci Dan takarar Gwamna. Amma abun ban mamaki jam’iyar PDP ko Dan takarar Kansila ba ta tura ya wakilce ta ba. Wanda na tabbatar, babbar dama ce, wannan Kungiyar ta baiwa ‘yan takara na baje kolin manufofinsu nagari. Wanda na tabbatar duk Wanda ya halarta tare da ji ko sauraren yadda MUHAWARAR ta kaya sai ya ji so da shaukin wani Dan takarar da ya ke da manufofin kirki ya shige shi. Wannan Kenan!

Ba zan manta da Maganar wani jigo a jam’iyar ba, ranar na ke tambayarsa. Wai Hon. Ya Maganar PDP kun yi shiru ga dama kun samu, yanzu kafin APC ta dawo kan ganiyarta. Abun mamaki wai sai na ji ya na fadin sun fi son su ga Inda aka Kai karshe da APC tukun.

Anya! An taba yin bori da sanyin kafa?

Anya PDP kuna tunanen ku ci jahar Zamfara a haka?

Sai dai masu iya magana na cewa iya ruwa fitar da Kai.

Abdulmalik Saidu Mai Biredi Tashar Bagu Gusau

The post Ko APC ba zatai takara ba PDP ba zata Iya cin Zamfara ba – Abdulmalik Gusau appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here