Sama da Shekaru 2: Hukumomin Dake Karkashin Ma’aikatar Cikin Gida Sun Koka Kan Rashin Karin Albashi

 

Hukumomin dake karkashin ma’aikatar cikin gida, wanda suka hada da NIS, NSCDC, FFS da NCS sun koka kan yadda maganar karin albashinsu taki ci taki cinyewa, inda suke korafin cewa rayuwar tana musu wahala musamman duba da yadda sauran jami’ai yan uwansu, kamar ‘Yan Sanda, Kwastam, DSS da EFCC, sukayi musu fintinkau a harkar albashi,

Jami’ an sun ce an dade ana ja musu rai akan karin, yayin da ko yaushe ake nuna musu yau ko gobe, a haka suka shafe tsawon shekaru biyu (2) da wani abu suna jiran gawon shanu.

A baya-bayannan ne, daf da karewar shekarar 2022 akayi zama da hukumar kudi da tsare-tsare (ministry of finance)akan yadda za’a daidaita albashin nasu da hukumar ‘Yan sanda, har aka fitar da jawabai kan cewa, zaa biyasu sabon tsarin albashin da yake dauke da karin kaso 40% na albashin nasu a karshen December, ta 2022

Sannan a watan January kuma za’ a biyasu arreas na wata 3, amma dai har yanzu shiru sukeji kamar an shuka dusa, bayan haka yanzu akayi maganar karin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya, a karshen watan Aprilu, sai gashi shima Karin ya bayyana babu wadannan jami’ai.

#Shin laifi ne ka zama a karkashin ita wannan ministry
#shin laifi ne ka zama dan kasa nagari
#ko aikin na sune bashi da muhimmanci ga alumma ko ga gwamnatin tarayya

Akarshe muna rokon gwamnati da ta duba alamarin wadannan jami’ai masu yi mata hidima babu dare babu rana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here