Farfasa Khalifa Dikwa ya Koka da Rashin Tsaro a Borno

 

Mamba a kungiyar dattawan Borno, Farfesa Khalifa Dikwa ya koka a kan tsanantar rashin tsaro a Borno.

Ya tabbatar da cewa babu wani gari a jihar baya da Maiduguri da ke da tsaro a dukkan jihar Borno.

Ya koka da rashin jin shawarar soji a yayin da suka kwato wasu garuruwa a 2014, hakan ne ya kawo abinda jihar ke ciki yanzu.

Farfesa Khalifa Dikwa, daya daga cikin dattawa a kungiyar dattawan Borno ya nuna damuwarsa a kan hauhawar rashin tsaro a yankin.

Ya ce baya da babban birnin jihar Borno, babu inda mutane ke rayuwa da tsaro a fadin jihar.

“Ko da a ce babu Boko Haram a wasu wurare, sun riga sun tsorata jama’a kuma suna zukatan jama’a tare da hana su zaman lafiya,” Dikwa ya sanar da Channels TV a wani shirin daren ranar Litinin.

“Lokaci zuwa lokaci suke shigowa a baburansu su zo suna hantarar jama’a har su biya haraji. Suna kai hari a kowanne lokaci.”

a yi ikirarin cewa dakarun sojin Najeriya basu ji shawarar da aka basu ta zama a dukkan iyakokin tudu na kasar nan bayan sun tarwatsa Boko Haram a 2014.

“A lokacin, PMC ta ce toh mun yi iyakar kokarinmu sauran ya rage na siyasa ne. Ku tattauna da ‘yan ta’adda domin kara samun karfin tsaro,” Malamin jami’ar yace.

“Kuma ku bar sauran jami’an tsaro su mamaye inda kuka kwace. Ku bar sojoji su tsaya a iyakokin tudu na kasarku.”

Farfesa Dikwa wanda ya bukaci jami’an tsaro su hada kansu wurin yakar ta’addanci, ya ce dakarun soji kadai ba za su iya yakar ta’addanci ba a jihar Borno.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here