Cutar Kolera ta Kashe Mutane 430 a Sudan

 

Fiye da mutum 430 ne suka mutu sakamakon annobar kolera a ƴan watannin da suka gabata, a daidai lokacin da yaƙin basasar ƙasar ke ci gaba a ƙasar, in ji ma’aikatar lafiyar ƙasar.

Alƙaluman waɗanda suka kamu da cutar sun ƙaru zuwa kusan 14,000 kamar yadda ma’aikatar lafiyar ƙasar ta sanar.

Sanarwar ta ce gwamnati na yin duk abin d aya kamata wajen “daƙile annobar a jihohin da annobar ta ɓarke.”

Rikicin da ke wakana a Sudan ɗin na matuƙar shafar samar da magunguna ga waɗanda abin ya shafa. Rikicin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 150,000 tun bayan fara yaƙin a bara kamar yadda wakilin Amurka na musamman a Sudan, Tom Perriello ya sanar.

Likitocin ƙasa da ƙasa sun ce “suna samun matsala daga dukkannin ɓangarorin biyu masu yaƙi da juna, abin da ya sa ayyukan jinƙai suka gaza samun masu buƙata.”

Ministan Lafiyar ƙasar, Haitham Mohammed Ibrahim ya ayyana ɓarekewar kolerar ne a tsakiyar watan Agusta.

Baya ga yaƙin da ake yi, ruwan sama da ambaliya da suka janyo cunkoso a sansanoni sun taimaka wajen ɓarkewar cutar ta kolera,

Esperanza Santos, jagoran ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa a Sudan ya ce “waɗannan abubuwa su ne suka haɗu suka haifar da annobar.

A wasu yankunan ma an umarci makarantu da kasuwanni da shaguna da su rufe domin daƙile yaɗuwar annobar.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here