‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Jahar Zamfara Sun Kona Gidan Kakakin Majalisar Dokokin Jahar
Yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Zurmi a jahar Zamfara.
Sun kona gidajen mutane amma ba’a san adadin gidajen ba kawo yanzu.
Gidan Kakakin majalisar jahar na cikin wadanda aka kona.
Zamfara – Yan bindiga sun banka wuta gidan Kakakin majalisar dokokin jahar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, da sauran gidan mutane a karamar hukumar Zurmi ta jahar.
Read Also:
Shugaban kwamitin tsaro da hukunta yan bindiga na majalisar, Abdullahi Shinkafi, ya tabbatar da hakan ranar Litinin.
Ya ce yan bindiga sun kai hari garin ne kuma suka banka wuta wasu gidaje, rahoton Tribune.
A cewarsa, wannan ya faru ne sakamakon artabun da Sojoji ke yi da yan bindiga a Zurmi.
Shugaban kwamitin wanda ya ziyarci wajen domin ganin abinda ya faru, yace gwamnati na son taimakawa mutanen da harin ya shafa da kuma tura karin jami’an tsaro.
Duk da cewa bai bayyana ko an yi rashin rayuka ba, ya ce an damke masu kaiwa yan bindigan abinci da man fetur biyu.
Ya ce yan bindigan sun yi amfani da kwale-kwale wajen tafiyar da kaya daga Sokoto zuwa karamar hukumar Shinkafi a jahar Zamfara.