Rikicin Jos: An Kona Shaguna 14 da Masallatai 2
Rikicin jahar Plateau ya ki ci, ya ki cinyewa har yanzu.
Bayan kisan kimanin mutane 35 a garin Yelwa, wasu sun kai hari kasuwa.
Sun kona Masallatai biyu tare da shagunan mutane duk da dokar ta baci da aka sanya.
Read Also:
Jos – Wasu fusatattun matasa sun kona Masallatai biyu tare da kona shaguna 14 a kasuwar kayan gine-gine dake karamar hukumar Jos ta kudu a jahar Plateau.
A cewar Daily Nigerian, shugaban masu sayar da kayan miya a kasuwannin jahar, Dalyop Pwasa, ya tabbatar da hakan.
Yace:
“Da gaske ne cewa wasu mutane sun shiga kasuwarmu ranar Laraba, sun fasa wasu shaguna, sun sace kayayyaki kuma sun kona shaguna 14.”
“Sun lalata Masallatai biyu dake cikin kasuwar.”
ALLAH ubangiji ya kawo mana zaman lafiya a kasar mu najeriya.Ameen ya Allah.