Sakamakon Zaben Shugabanni: Jam’iyyar APC ta Samu Korafi Daga Jahohi 14

 

Jam’iyyar APC ta samu korafe-korafe daga zabukan mazabu da aka gudanar.

Mai Mala Buni ya kafa kwamitocin da za su saurari karar da aka kai gabansa.

Wannan zai jawo karin bata lokaci wajen shirya zabukan kananan hukumomi.

An samu korafe-korafe a sakamakon zabukan shugabanni da jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar kwanaki a mazabun da ke jahohin fadin kasar nan.

Jaridar The Nation ta ce jam’iyyar APC ta samu korafi daga jahohi akalla 14, inda wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar suka kai kararsu gaban kwamitin rikon kwarya.

Rahoton ya ce jahohi 12 ba su gabatar da rahoton zabukan da aka yi ga kwamitin Mai Mala Buni ba.

Ana tunanin cewa idan ba a kammala maganar zabukan mazabu ba, ba za a sa ranar da za a gudanar da zaben shugabanni na kananan hukumomi ba.

Jam’iyyar APC ta kafa wasu kwamitoci da za su saurari korafin da aka gabatar. An rantsar da wadannan kwamitoci ne a ranar 12 ga watan Agusta, 2021.

Shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni, ya rantsar da wadannan kwamitoci masu dauke da mutane biyar a sakatariyar APC a birnin tarayya, Abuja.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here