An Kori ‘Yan Sanda Uku da ke yi wa Rarara Rakiya

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kori wasu jami’anta uku daga aiki bayan ta same su da laifukan rashin ɗa’a.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce an samu ‘yan sandan ne da aikata abubuwan da ka iya zubar da mutuncin rundunar inda suka yi amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba, da tozarta muƙaminsu, da nuna tsagwaron rashin ɗa’a, da kuma ɓarnata harsasan gaske.

Ta ce ‘yan sandan suna aiki ne da wani mawaƙi a Kano lokacin da aka tura su don ayyukan rakiya da bayar da kariya.

Ta ce matakin na zuwa ne bayan ƙorafe-ƙorafe da kuma binciken da aka yi kan wata shaidar bidiyo da aka yayata sosai ranar 7 ga watan Afrilun 2023 a shafukan sada zumunta.

A cewarta, an zargi ‘yan sandan uku – na sashen ba da kariya ta musamman (SPU) da suka haɗar da Sufeto Ɗahiru Shu’aibu da Saje Abdullahi Badamasi da Saje Isah Ɗanladi – da zafin hannu, da halayyar rashin ƙwarewa, da amfani da makami ta hanyar da ba ta dace ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here