Sayar wa da Rasha Makamai: Koriya ta Arewa ta Musanta Jita-Jitar

 

Koriya ta Arewa ta ce bata taba sayar wa da Rasha makamai ba, kuma ba tada shirin yin haka a nan gaba.

Gwamnati a Pyonyang na martani ne ga zargin Amurka na cewa Rasha na mayar da hankali ne Koriya ta Arewa wurin sayen makamai.

Pyonyang kuma a martanin ta zargi Amurka da ire-irenta da yada jita-jita ”don cimma farfagandar siyasa da ta sojinta”.

A farkon watan Satumba ne ofishin harkokin wajen Amurka ya zargi Koriya ta Arewa da amincewa ta sayar wa Rasha makamai, da suka hada da rokoki da sauran makamai masu linzami.

To amma ta ce ba bu shaidar cewa za a yi amfani da su ne a yakin Ukraine.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here