Yaduwar Korona: Gwamnatin Legas ta Saka Sabuwar Doka Kan Masu Biki

 

A sabuwar dokar gwamnatin Lagas sai sabbin ma’aurata sun nemi izini kafin su tara jama’a a wajen biki.

Hakan na daga cikin matakan yaki da annobar korona.

Daga yanzu mutane 300 ne kadai za su halarci taron biki kuma sai sun kiyaye dokokin dakile cutar.

Gwamnatin jihar Lagas ta kafa wata sabuwar doka da ya gindayawa sabbin ma’aurata neman izini daga gareta kafin kafin su tara jama’a domin yin shagalin biki.

Wannan sabon matakin yana kunshe ne a cikin wani bayani da gwamnatin ta fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Disamba mai taken “Ku zauna a gida.”

Wani bangare na jawabin na cewa:

“Bikin aure da kum taron jama’a kar su wace 300 bayan an samu amincewar hukumar kiyaye lafiya ta jihar Lagas.”

Shugaban hukumar kariya ta jihar Lagas, Lanre Mojola, ya bayyana cewa neman izinin kyauta ne, inda sabbin ma’auratan za su je shafin hukumar domin yin rijista.

Ya kara da cewa jami’an kiyaye lafiya za su je wuraren taron domin tabbatar da cewa an bi ka’idojin kare kai daga kamuwa da cutar korona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here