Yaduwar Cutar Korona: Adadin Mutanen da Suka Kamu Cikin Kwana Uku

 

Ko shakka babu yanzu, an shiga babin annobar korona 2.0.

Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a ‘yan kwanakin baya bayan nan.

Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa kuma an dakatad da bukukuwan Kirismeti.

Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu an koma gidan jiya.

Mutane 1041 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Alhamis, 24 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 81,963 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 69,651 yayinda 1242 suka rigamu gidan gaskiya. Daga ranar Talata zuwa yanzu, sama da mutane 3000 suka kamu a Najeriya.

Ga jerin jihohi da adadin da suka kamu:

Lagos-316

FCT-210

Kaduna-83

Plateau-70

Gombe-56

Oyo-56

Katsina-47

Nasarawa-35

Kano-33

Ogun-21

Rivers-17

Niger-14

Imo-14

Delta-12

Kwara-12

Edo-12

Benue-9

Anambra-8

Taraba-4

Ekiti-4

Ebonyi-6

Bayelsa-1

Sokoto-1

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here