Cutar Corona ta yi Silar Mutuwar Wani Babban Kwamandan Sojoji
Cutar korona ta yi sanadiyar rasuwar babban kwamandan Sojojin Najeriya, Irefin.
Irefin ya fara rashin lafiya ne bayan ya halarci taron hafsoshin sojoji da ke gudana a Abuja.
Rundunar soji ta dakatar da taron ta kuma bukaci mahalarta taron su killace kansu na kwanaki 14,
Read Also:
Irefin, Manjo janar kuma babban kwamandan six division na sojin Najeriya ta jihar Rivers ya rasu sakamakon kamuwa da Covid 19.
Kwamandan yana daga cikin mahalarta taron hafsoshin sojoji da ke gudana a Abuja kafin ya kamu da rashin lafiyar ya rasu, The Cable ta ruwaito.
An soke taron sakamakon kamuwa da korona da wasu mahalarta taron suka yi cikinsu har da kwamandojin da shugabannin makarantun sojoji.
An bukaci dukkan mahalarta taron su killace kansu na kwanaki 14.
Cikakken rahoton na zuwa …