Ranar da Kotu zata Bada Belin Ndume
Alkalin babbar kotun tarayya ta Abuja, Okon Abang ya tsayar da ranar Juma’a don yanke hukunci kan bukatar belin Ndume.
Abang dai ya tsare Ndume a gidan maza tun ranar Litinin bayan ya kasa gabatar da Abdulrasheed Maina a gabansa.
Sanatan shine ya tsayawa tsohon shugaban na hukumar fansho a matsayin jingina a shari’arsa da EFCC.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta tsayar da ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, domin zartar da hukunci a kan bukatar bayar da belin Sanata mai wakiltan Borno ta Kudu, Ali Ndume, Channels TV ta ruwaito.
An dai tsare Ndume a gidan yarin Kuje tun a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba, kan tsayawa Abdulrasheed Maina da yayi a matsayin jingina inda shi kuma ya tsere.
Read Also:
Justis Okon Abang a ranar Alhamis, ya dage zaman yanke hukuncin bayan lauyan Sanata Ndume, Marcel Oru, ya yi muhawara kan bukatar belin, inda shi kuma lauyan hukumar yaki da rashawa, Mohammed Abubakar ya nuna adawa.
Maina, wanda ya kasance tsohon shugaban hukumar fansho na fuskantar shari’a kan wasu tuhume-tuhume na zambar kudade har naira biliyan biyu da EFCC ke yi masa.
Justis Abang ya soke belin da aka ba Maina a ranar 18 ga watan Nuwamban 2020, sannan yayi izinin kama shi, da kuma umurnin ci gaba da shari’a a bayan idonsa.
Alkalin ya kuma tsare Sanata Ndume a gidan maza har sai ya gabatar da Maina ko kuma ya biya kudi naira miliyan 500 na yarjejeniyar belin zuwa asusun tarayya.
A ranar Talata ne Ndume ta hannun lauyansa, ya daukaka kara a kan umurnin tsare shi a gaban kotun daukaka kara, tare da takardar neman a bayar da belinsa a gaban Abang.