Kotu ta Bayar da Belin Tsohon Gwamnan CBN, Emefiele
Mai sharia’a Olukayode Adeniyi na babbar kotun tarayya da ke Abuja a Najeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Read Also:
Alƙalin ya bayar da umarnin sakin Emefiele nan take ga lauyoyinsa, waɗanda aka ɗora wa alhakin kai shi kotu a zaman da za a yi a makon gobe da kuma duk lokacin da ake buƙata.
Alƙalin ya kuma ce wajibi ne ga tsohon shugaban bankin na CBN ya ajiye dukkanin takardun tafiye-tafiyensa a hannun magatakardar kotun kafin shari’ar ta kankama.
Haka nan ta kuma ce dole ne a daina tsare shi ba tare da shari’a ba.
Kotun ta ce ba za ta kawar da idonta daga batun cewa ya shafe kwana 151 a tsare ba, kuma kotun ta ce dole ne gwamnatin tarayya da ministan shari’a su martaba umarnin kotu.