Kotu ta Bukaci Hon. ‘Dan Galadima
Lauyan EFCC yana neman Kotu ta daure Sani Umar Dan-Galadima a kurkuku.
Sani Umar Dan-Galadima shi ne wanda ya tsaya wa Faisal Abdulrasheed Maina.
‘Dan Majalisar yana cikin barazanar rasa N60m ko a garkame shi a gidan yari.
Babban kotun tarayya da ke zama a Abuja ya na neman ‘dan majalisa Sani Umar Dan-Galadima ya bayyana a shari’ar Alhaji Abdulrasheed Maina.
A ranar Talata, 24 ga watan Nuwamba, 2020, Alkali mai shari’a Okon Abang ya yanke hukunci cewa dole Sani Umar Dan-Galadima ya zo kotu gobe.
Okon Abang ya na son ganin Honarabul Sani Umar Dan-Galadima ne a ranar Laraba, idan bai yi hakan ba, zai bada umarnin jami’an tsaro su kama shi.
Bayan haka, dazu jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Alkalin ya bada umarnin a kamo masa yaron wanda ake tuhuma, Faisal Abdulrasheed Maina.
Read Also:
Hukumar EFCC ta dogara da sashe 354 (2) na dokar ACJA, ta nemi Alkali ya cigaba da shari’a a kan Faisal Maina ko da ba a ga fuskarsa a cikin kotu ba.
‘Dan-Galadima mai wakiltar mazabar Kauran Namoda, jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP ne tsaya wa Faisal Abdulrasheed Maina a gaban kuliya.
Idan ba haka ba, ‘dan siyasar zai iya rasa kudinsa Naira miliyan 60 a hannun gwamnatin tarayya.
Lauyan EFCC, Barista M.S. Abubakar ya sanar da kotu cewa ba a ga keyar Faisal Maina da wanda ya tsaya masa ba, don haka ya nemi a soke belin da aka basu.
Abubakar ya na so a aika ‘dan majalisar zuwa gidan yari ko kuma ya hakura da kudin da ya bada.
A yau kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya kwana a gidan gyaran hali na Kuje, Abuja bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja a shari’ar Abdulrasheed Maina.
Sanatan ya ce zai daukaka kara akan hukunci da aka yanke masa yau domin ya samu ‘yanci.