Kotu ta Daga ƙarar da ke Cewa Atiku ba ‘Dan Najeriya Bane
Kotu ta yi zama kan bukatar a hana Atiku tsayawa takarar shugaban kasa 2023, an kuma dage kara.
Rahotanni sun bayyana cewa, an dage karar ne bisa gazawar bangaorori wajen bijiro da wasu bayanai.
Wata kungiya ce ta shigar da Atiku kara kan cewa shi ba dan Najeriya, don haka bai cancanci tsayawa takara ba.
Abuja – Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar ya nuna cewa an dage karar da ke neman kalubalantar cancantar tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasan Najeriya a ranar Litinin, 27 ga watan Satumba.
Read Also:
A cewar mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, hakan ya faru ne saboda gazawar bangarorin karar wajen daidaita tsare-tsaren da aka yi musu kwaskwarima don karbar wanda ake kara na 5.
Vanguard ta kara da cewa alkalin a hukuncin da ya yanke ya dage shari’ar har zuwa ranar 6 ga watan Disamba don ci gaba da shari’a.
Idan za a iya tunawa, gamayyar Incorporated Trustees of Egalitarian Mission for Africa (EMA) sun yi karar Atiku ba haifaffen Najeriya bane, don haka bai cancanci tsayawa takara a Najeriya ba.
Kungiyar ta sanya tsohon mataimakin shugaban kasa da kuma jam’iyyar PDP, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 4.