Dokokin Kayyade Kayan Aure a Gumel Dake Jahar Jigawa

 

An kafa dokokin kayyade kayan aure a wata Masarauta dake jahar Jigawa.

Daga cikin dokokin an hana yin ‘Gara’ kuma lefe kada ya wuce N100,000.

Hakazalika an hana yin taro irinsu Kauye Day, Arabian Night, da sauransu.

Jigawa – Masarautar Gumel ta kafa sababbin dokoki kayyade kayan aure a yankinta domin saukakawa matasa aure sakamakon halin da al’umma ke fama da shi.

A takardar mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar kuma Maji Dadin Gumel, Alhaji Murtala Aliyu, an umurci Limaman Juma’a Masarautar su fadakar da al’umma kan wannan sabuwar doka.

Masarautar tace ta kafa dokokin ne domin saukake wahalhalu da tsada da al’adu dake tattare lamuran daurin aure.

Dokoki nawa ne aka kafa?

A kwafin dokokin da masarautar ta hadawa Limaman, an ga jerin dokokin 19 da suka bayyana abubuwan da ya kamata Saurayi mai niyyar aure ya tanada.

Daga cikin Masarautar ta lissafa adadin abubuwan mutum zai saya da kuma abubuwan da ba zai saya ba.

Hakazlika an hana wasu tsare-tsare da bukukuwa da aka saba yi irinsu ranar Kauyawa da sauransu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here