Sojojin Chadi na Saida Makamai a Kan $20 Idan Suna Neman Kudi – Awwal Gambo

 

Shugaban hafsun sojan ruwa ya zargi sojojin wasu kasashe da saida makamai.

Awwal Gambo ya yi wannan bayani a lokacin da ya bayyana a zauren majalisa.

Gambo yace sojojin Chadi na saida makamai a kan $20 idan suna neman kudi.

FCT, Abuja – Daily Trust tace rundunar sojojin ruwan Najeriya ta zargi sojojin kasar Chadi da laifin saida kananan makamai ta hanyar da ba ta dace ba.

Shugaban hafsun sojan ruwa na kasar nan, Awwal Gambo ya bayyana wannan a lokacin da ya bayyana a gaban zauren majalisar wakilan tarayya.

Commodore Jemila Abubakar tayi wannan bayani da ta wakilci shugaban hafsun sojin ruwan wajen sauraron wasu kudiri da aka gabatar a majalisa.

Jaridar tace ‘yan majalisar tarayya sun kawo wasu kudirori da ake sa rai za su takaita yaduwar kananan makamai a Najeriya domin samun zaman lafiya.

Jemila Abubakar ta shaida wa majalisar wakilan cewa makaman da suke yawo a wasu kasashe suna kawo masu cikas wajen yakar matsalar rashin tsaro.

Me Commodore Jemila Abubakar ta fada wa Majalisa?

“Na jagoranci yakin Boko Haram, kuma zan iya fada maku cewa wasu kasashe ba su da gidan makamai.” “Ba su da gidajen makamai, saboda haka ana ba su gudumuwar makamai ne.

Bana so in fadi sunayen kasashen – Amma kasashe masu taso wa da suke taimaka mana, suna kara kawo mana cikas a Najeriya.”

“Saboda za ka ga sojan Chad yana da makamai 20 zuwa 30 a karkashin gadonsa. Da zarar ya rasa kudi, sai ya fito da su ya saida a kan $20 ko $30.”

Da take jawabi, Commodore Jemila Abubakar tace akwai bukatar a hada-kai da ECOWAS domin a kawo dokar yadda za a rika amfani da makamai a Afrika.

Idan zargin da babbar jami’ar sojar ta Najeriya ta jefi sojojin kasar Chadi sun tabbata, farashin abin da ake saida bindiga a makwabtan bai wuce N12, 000 ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here