Kotu ta Dage Sauraron Shari’ar ‘Dan China da ya Kashe Budurwarsa a Kano

 

Babbar kotun jihar Kano ta dage sauraron shari’ar dan China, Geng Quangrong, wanda ake zargi da kashe budurwarsa yar Kano.

Justis Sanusi Ado Ma’aji ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Oktoba saboda rashin lauya da zai kare wanda ake tuhuma.

Saboda girman laifin da ake tuhumarsa a kai, alkalin ya amsa rokon Mista Geng na neman a bashi dage shari’a don ya kira lauyansa da zai kare shi.

Kano – Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Justis Sanusi Ado Ma’aji ta dage sauraron karar dan kasar China, Geng Quangrong, wanda ake zargi da kashe masoyiyarsa yar Najeriya, Ummukulsum Sani Buhari.

Daily Trust ta rahoto cewa an dage zaman ne saboda rashin zuwan lauyan da zai kare wanda ake zargin.

A yayin zaman na ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, Quarong, ya roki kotu da ta dage zaman domin bashi damar kiran lauyansa da zai tsaya masa.

Da yake martani, Atoni Janar na jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan bai nuna adawa da rokon wanda ake kara ba na neman a dage shari’ar.

Ya ce:

“Lallai wannan shari’ar ba zai ci gaba ba a yau ba tare da lauya da ke kare wanda ake zargi ba. Laifin da ake tuhumarsa a kai babban lamari ne. A cikin wannan hali, muna neman a dan dage sauraron karar don baiwa wanda ake zargi damar samun lauya.”

Justis Ma’aji ya dage sauraron shari’ar zuwa 4 ga watan Oktoba, rahoton Aminiya.

Ana dai zargin Mista Geng da kashe Ummitah, matashiya mai shekaru 23. Marigayiyar da wanda ake zargin suna soyayya da junansu kafin alakarsu tayi tsami.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here