Ba Zai Yiwu Gwamnatin Buhari ta ba ASUU Abin da Babu Shi ba, Don Haka su yi Hakuri –  Ngige

 

Yayin da yajin aikin ASUU ke kara kamari, gwamnatin Najeriya na ta tunanin hanyoyin da za a kawo.

mafita Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya magantu da ASUU, ya roki su gaggauta janye yajin aiki.

Ministan kwadago ya ce ba zai yiwu gwamnatin Buhari ta ba ASUU abin da babu shi ba, don haka su yi hakuri.

FTC, Abuja Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai a Najeriya ya yi kira ga kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU da su duba tare da janye yajin aiki saboda biyan muradan dalibai a kasar.

Ya bayyana hakan ne yayin dagawa da ASUU, ministan kwadago Chris Ngige da mukaddashin akanta janar na kasa Okolieaboh Sylva a jiya Alhamis 29 ga watan Satumba.

Kakakin na majalisa ya ce an biya bukatar majalisar a yanzu kam, TheCable ta ruwaito.

A kalamansa:

“Ba zai yiwu a ce kowa ya yi kuskure ba. Muna tafiya kan abin da muka ce a zamanmu na karshe, don Allah saboda muradin ‘ya’yanmu, muna rokonku ba wai don umarnin kotu ba.”

Gbajabiamila ya ce ana yin mai yiwuwa domin ganin an tabbatar da warware batutuwan da suka shafi tsarin biyan albashin UTAS da ASUU ta ke son amfani dashi.

Ya kuma ce ya fahimci ba suna fushi ne don karan kansu ba, suna yi ne domin kawo mafita ga ‘yan baya.

Ku karbi tsarin albashin bai daya na IPPIS

Shi kuwa da yake magana, mukaddashin akanta janar na kasa ya roki ASUU da su runguma tare da amince da tsarin albashin gwamnati na IPPIS.

Ya kuma bayyana cewa, idan ma akwai wata bukata ta kudaden alawus-alawus, ofishinsa zai tabbatar da ba ASUU wadannan bukatu.

Ya shaidawa ASUU cewa:

“Ya kamata mu zauna mu san wadannan abubuwan kuma mu magance a cikin IPPIS. Za mu gyara duk inda muka yi kuskure yanzu.”

“Idan muka amince da batun ASUU, zai ba da kofa ga sauran ma’aikata su ce a basu damar kawo hanyar albashinsu, sojoji da ma’aikatan lafiya duk a kan IPPIS suke, ya kamata ASUU ta zauna damu da ga irin ci gaban da muka samar.”

Ya kuma ce babu wata matsala idan ASUU ta amince da karbar tsarin biyan albashin na IPPIS.

Gwamnati ba za ta ba ASUU babu ba, inji Ngige

A nasa jawabin, ministan kwadago Ngige ya ce gwamnatin tarayya ba za ta ba ASUU abin da bata dashi ba.

Ministan ya ce, tun farko ya zo tabbatar da amfani da UTAS da sauran hanyoyin biyan albashi guda biyu da ASUU ta kawo.

Sai dai, a cewar Ngige, dukkan hanyoyin da ASUU ta kawo sun gaza tsallake tantancewar da aka gwada su a kai.

Da yake martani, shugaban ASUU, Emmaneul Osodeke ya ce, yana matukar ciwo ganin yadda ‘yan Najeriya suka gaza fahimtar yadda tsarin jami’o’i ke tafiya.

 

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here