Kotu ta Dakatar da Kwamitin Rikon Kwarya na Jam’iyyar PDP a Jahar Ebonyi
Har yanzu PDP bata kashe wutar rikicin shugabancinta da ke ruruwa ba a jahar Ebonyi.
Hakan ya kasance ne yayinda kotu ta dakatar da kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar a ranar Laraba.
An kuma rushe kwamitin karkashin jagorancin Fred Udogu yayinda kotu ta bayyana ta a matsayin wacce bata bisa ka’ida.
Kotu ta kori Fred Udogu, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jahar Ebonyi.
A hukuncin da ta yanke a ranar Laraba, 10 ga watan Fabrairu, wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abaliki, babban birnin jahar, ta kuma bayyana kwamitin PDP karkashin jagorancin Udogu, a matsayin wace bata bisa ka’ida.
Read Also:
Nnachi Okoro, lauyan PDP na bangaren da Onyekachi Nwebonyu ke jagoranta a jahar Ebonyi ya shigar da kara a gaban kotu a watan Nuwamban 2020, yana me neman a rusa bangaren da Udogu ke jagoranta.
Mai shigar da karar ya kuma bukaci kotun da ta dawo da shi a matsayin lauyan PDP reshen Ebonyi ba tare da sauraran ta bakin kowani bangare ba.
Yana mai bayyana cire shi da aka yi bayan ficewar Gwamna Dave Umahi a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulki.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Jastis Aluko Akintayo, a cikin hukuncin awanni uku ya yi ikirarin cewa cire Okoro ya saba wa doka sannan ya ba da umarnin a mayar da shi.
Ya kuma umarci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da kar ta amince da kwamitin rikon kwarya da shugabancin PDP na kasa ya kafa a Ebonyi.
Mai Shari’a Akintayo ya kuma yanke hukuncin cewa jam’iyyar PDP ta kasa ta gaza gabatar da hujja gaban kotu game da zargin cin amanar jam’iyya da kokarin rusata da take yi wa shugabancin kwamitin jam’iyyar na jahar Ebonyi.