Bayan Nada Sabon Shugaba a PDP: Kotu ta Dawo da Secondus Kan Kujerarsa

 

Wata babbar kotu a jahar Kebbi ta soke umarnin dakatarwa, tace Uche Secondus ya koma kan kujerarsa ta shugaban PDP.

Alkalin kotun, mai shari’a Nusrat Umar, itace ta bayyana haka bayan ta saurarin karar a Birnin Kebbi.

Wannan umarnin na zuwa awanni kaɗan bayan jiga-jigan PDP sun yanke hukuncin ɗora shugaban riko.

Abuja – Wata babbar kotu a jahar Kebbi ta bada umarnin cewa Prince Uche Secondus ya koma matsayinsa na shugaban jam’iyyar PDP na kasa, kamar yadda the nation ta rawaito.

Alkalin kotun, Mai shari’a Nusrat Umar, ita ce ta bada wannan umarnin bayan shigar da kara gabanta a Birnin Kebbi, babbar birnin jahar.

A karar da aka shigar gaban kotun, wadda akaiwa lamba KB/AC/M. 170/2021, mai shari’a Nusrat tace ta gamsu sosai bayan karanta rantsuwar wanda ake karewa.

Umarnin kotu kan Secondus

Umarnin da kotun ta bayar yace:

“Kotu ta bada umarnin wanda aka shigar kara na farko, Uche Secundus, ya cigaba da aikinsa na shugabancin jam’iyyar PDP ta kasa kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin Najeriya (1999 wanda aka yiwa garambawul)”.

“Da kundin dokokin jam’iyyar PDP yayin da za’a cigaba da sauraron karar har zuwa hukuncin karshe.”

“Wannan kotu ka iya sake bada wani umarnin idan bukatar hakan ta taso nan gaba.”

Wasu mambobin jam’iyyar PDP, Yahaya Usman, Abubakar Mohammed da kuma Bashar Suleman, sune suka shigar da kara gaban kotu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here