Kotu ta Hana EFCC Takardar Izinin Cafke Diezani Alison-Madueke

Babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, ta ki amince da bukatar hukumar EFCC na ba da izinin cafke Diezani Alison-Madueke

An dage sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Disamba 2020, domin tattara hujjoji tare da gurfanar da wacce ake karar gaban kotu – EFCC ta maka tsohuwar ministar albarkatun man fetur a kotu ne akan zarginta da ba hukumar INEC cin hancin N362m don yin magudi a zaben 2015 Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja ta hana takardar amincewa hukumar EFCC izinin cafke Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur.

Ijeoma Ojukwu, mai shari’ar, ta ki amincewa da bukatar EFCC ne saboda gazawar hukumar na gabatarwa kotun shaidar kotu na kiranye ga ministar a baya. Ta ce ya zama wajibi a gabatarwa kotu takardar shaidar goron gayyatar kotu ga tsohuwar ministar, kafin kotun ta amince ta bayar da izinin cafke Alison-Madueke.

Mai shari’ar ta ce, bayar da takardar goron gayyata ga mutum, ba takardar banza bace, dole EFCC ta gabatar da makamanciyar takardar da kotun ta aikawa Alison.

Hukumar EFCC ta shaidawa kotun cewa ofishin Antoni Janar na kasa da ma’aikatar shari’a na bbukatar izinin cafke tsohuwar ministar ne, don samun damar dawowa da ita kasar.

“Tuni na bi diddigin bukatar mai shigar da karar. Umurnin kotu na farko da ta bayar ya ci karo ne da sashe na 831 na dokar ACJA,” a cewar mai shari’ar.

“Ya zama nawa nazarin cewa takardun goron gayyatar da muka aikawa wacce ake tuhumar zai taimaka wajen zama hujja ga ofishin AGF.

“A yau, wacce ake tuhumar ba ta cikin kotu kuma ba a bayar da dalili ba. An sanar da ni cewa, ana da yakinin cewa, wacce ake tuhumar yanzu haka tana kasar Burtaniya. “Haka zalika, muna da rahoton cewa yunkurin hukuncin kan mai laifin ya ci tura sakamakon rashin kasancewar izinin cafke wacce ake zargi.

“Amma idan haka ne, ya kamata bangaren da ke kara su mika bukatar neman izinin tare da hujjoji daga ofishin Antoni na kasa. “Da wannan, na ke ba ku lokaci domin ganin cewa kun aikata komai akan doka da oda.”

A ranar 24 ga watan Yuni, ta bayar da takardar goron gayyata ga tsohuwar ministar, domin fara sauraron karar da aka shigar a kanta a ranar 28 ga watan Oktoba 2020. Sai dai, a ranar da aka dawo ci gaba da sauraron wannan shari’ar, Diezani ba ta halarci zaman kotun ba. An dage sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Disamba 2020, domin tattara hujjoji tare da gurfanar da wacce ake karar gaban kotu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here