Kotun Jahar Legas ta Garkame Mata Mai Shekaru 55 Bisa Zargin ta da Marin Jami’in ɗan Sanda
Wata kotu dake zamanta a Ikeja, babban birnin jahar Lagos, ta garkame wata mata yar kimanin shekara 55 bisa zargin faɗa da ɗan sanda.
Maria Taiwo, ta tafka wa wani sajan ɗin yan sanda mari yayin da suke gardama a caji ofis biyo bayan kame ɗan ta da suka yi.
Sai dai kotun ta bada belin matar a kan kuɗi naira dubu N100,000, sannan kuma ta ɗage sauraron ƙarar zuwa watan Nuwamba.
Lagos – Kotun majistire dake zamanta a Ikeja, jahar Lagos, ta garkame wata mata yar kimanin shekara 55, Maria Taiwo, bisa zargin ta da marin jami’in ɗan sanda, kamar yadda Vanguard ta rawaito.
Yan sanda sun gurfanar da Taiwo mai sana’ar gyaran gashi a 23, Calvary St., Obawole, Ogba, Lagos, a gaban kotun kan zargin tada yamutsi da cin mutuncin ɗan sanda.
Read Also:
Mai shigar da kara, ƙaramin sufetan yan sanda, Olusegun Oke, ya shaidawa kotu cewa matar ta aikata laifin ne ranar 31 ga watan Agusta a caji ofis ɗin Ogba.
Meyasa matar ta aikata haka?
Bugu da ƙari, Oke ya faɗawa kotu cewa matar ta aikata haka ne a caji ofis ɗin da ake tsare da ɗan data haifa.
Yace cece-kuce ya ɓarke tsakanin matar da ɗaya daga cikin jami’an yan sandan ofishin, Sajan Ameh Elijah.
Laifin da Taiwo ta aikata, a cewar mai shigar da kara, ya saɓa wa kundin dokokin dake kunshe a sashi na 168 da 170 na dokikin aikata manyan laifuka a jahar Lagos.
Sai dai a nata ɓangaren, wacce ake ƙara, Maria Taiwo, tace sam ba ta aikata laifin da ake zarginta da shi ba.
Wane mataki Kotu ta ɗauka?
Majistire D.S Odukoya, ya baiwa wacce ake ƙara damar beli a kan kuɗi kimanin dubu N100,000.
Daga nan kuma sai Odukoya ya sanar da ɗage ƙarar har zuwa 3 ga watan Nuwamba, 2021.