Kotu ta Hana Bada Belin Wani Farfesa
Ignatius Uduk zai shafe akalla kwanaki biyar a gidan yari kafin ya samu beli.
Farfesan ya na kotu da hukumar EFCC ne bisa zargin hannu a magudin zabe.
Malamin makarantar ya karyata zargin da ake yi masa na murde zaben 2019.
A ranar Laraba ne Alkalin babban kotun tarayya da ke garin Uyo, Akwa Ibom, ya bukaci a tsare Farfesa Ignatius Uduk a gidan gyaran hali.
Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 9 ga watan Disamba, 2020, cewa Ignatius Uduk zai yi kwanaki biyar a tsare kafin ya iya samun beli.
Jaridar ta ce malamin makarantar zai san ko zai samu beli a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba.Kafin nan za a cigaba da tsare sa a kurkukun.
Read Also:
Hukumar zabe na kasa watau INEC, tana zargin Ignatius Uduk wanda ke koyar wa a jami’ar Uyo, Akwa Ibom da laifuffuka uku a gaban kotu.
Uduk ya musanya cewa ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su. Farfesan ya kuma bukaci a ba shi beli ta hannun lauyansa, Samuel Ndah.
Barista Samuel Ndah ya na neman beli ne ta sanayya, amma Lauyan da ya tsayawa hukumar INEC ya roki Alkali ya guji sakin Farfesa Uduk.
Lauyan da ya shigar da kara a madadin hukumar da ke gudanar da zabe a Najeriya ya ce bai dace a kyale Uduk ba, ya roki a cigaba da tsare shi.
Dalilin da INEC ta kafa shi ne Farfesan bai zo kotu ba har sai da ya ji an yi cigiya, za a kama shi.
Alkali mai shari’a A.E Archibong bai bada umarnin a saki malamin zaben ba, hakan ya na nufin zai cigaba da zaman gidan kaso har makon gobe.