Kotu ta Hana Majalisar Jahar Kano Kan Bincikar Muhuyi Magaji
Wata babbar kotun jahar Kano ta tsawatarwa majalisar jahar Kano kan bincikar Rimingado.
Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Sanusi Ma’aji ta ce sai ta kammala shari’ar kafin a cigaba.
Idan mun tuna, Muhuyi Magaji ya samu gayyata daga majalisar jahar kan wani koke da aka mika a kansa.
Wata babbar kotu a jahar Kano wacce ta samu shugabancin Mai Shari’a Sanusi Ma’aji, ta hana majalisar jahar Kano bincikar tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa, PCACC, Muhuyi Magaji, har sai an kammala shari’a.
Read Also:
Majalisar jahar Kano ta gayyaci Rimingado da ya bayyana gaban kwamitin wucin-gadi na majalisar domin bincikar korafin da aka kai na ranar Laraba, 14 ga watan Yulin 2021, Solacebase ta wallafa.
Amma Rimingado yayin dogaro da rashin lafiyar da yake fama da ita kuma ya bayyana bayanin likita a rubuce, ya bukaci asalin kwafin korafin da majalisar ta samu a kansa wanda hakan yasa ta bukaci ya bayyana a gabanta.
Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, kotun a ranar Juma’a, ta yanke wadannan hukuncin:
“Umarnin dakatar da bincike na wucingadi ya karbu inda aka bukaci kada a sake bincikar mai karar kan lamari mai alaka da hakan har sai kotu ta kammala shari’ar.
“Kotu ta bada umarnin a gaggauta jin shari’ar cikin lokaci.” Alkalin ya dage sauraron karad zuwa ranar 6 ga watan Augustan 2021.