Kotun Jahar Oyo ta Hana Hukumar Tsaro ta Farin Kaya Tursasa Bincike da Toshe Asusun Banki Igboho
Wata kotu a jahar Oyo ta umarci gwamnatin tarayya da ta dakata da kame Sunday Igboho.
Kotun ta bayyana haka ne a yau Laraba 4 ga watan Agusta, 2021 yayin zaman sauraran kara.
Sunday Igboho ya shigar da kara ne kan neman a karba masa diyyar miliyan 500 bisa shiga gidansa.
Read Also:
Mai shari’a Ladiean Akintola na babbar kotun Oyo ya hana hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da babban lauyan gwamnatin tarayya kamawa, bincika, tursasawa, da toshe asusun banki na Cif Sunday Adeyemo aka Sunday Igboho, The Nation ta ruwaito.
An bayar da wannan umurnin ne bayan wani tsohon kudiri da lauyansa Cif Yomi Aliu (SAN) ya gabatar a kotun a ranar Laraba. Wannan ya samo asali ne daga kudirin neman diyyar Naira biliyan 500 saboda mamaye gidansa da ke Ibadan, babban birnin jahar Oyo a ranar 1 ga watan Yuli.
Aliu ya bayyana kwarin gwiwa cewa AGF Abubakar Malami (SAN) ba zai yi watsi da umarnin kotu ba, yana mai jaddada cewa an bayar da umarnin ne kai tsaye kan ofishinsa.
An dage sauraren karar zuwa 18 ga watan Agusta.