Jigawa: Kotu ta Yanke wa Wanda ya yi wa Gwamnan Jahar Kazafi Hukuncin Zaman Gidan Yari

 

Kotu a Jihar Jigawa ta yanke wa wani mutum hukuncin zaman gidan yari saboda ɓata wa Gwamna Badaru suna.

Sabi’u Ibrahim Chamo ya yi ikirarin cewa Gwamna Badaru ya karbi kudin wasu yan APC da sunan zai basu tikitin takara.

Da aka gurfanar da shi a kotu, wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya ce bashi hujja kan iƙirarin da ya yi Alƙalin kotun majistare da ke zamanta a Jigawa ta yanke wa wani Sabi’u Ibrahim Chamo hukuncin gidan yari saboda ɓata sunan Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar.

An fara kama Mista Chamo ne a jajiberin ranar Kirsimeti sannan aka tsare shi kafin gurfanar da shi a gaban kotu bayan ya kasa bada hujja kan zargin da ya yi a Facebook, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mutumin da aka yanke wa hukuncin ya yi zargin cewa gwamnan ya yaudari masu neman takara da yawa a APC ta hanyar karbar kudinsu da nufin basu tikitin takara.

Yayin shari’ar, bayan karanto masa abinda ake zarginsa da aikatawa, Mista Chamo ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Daga nan, kotu ya yanke masa hukuncin watanni shida a gidan yari da zabin biyan tarar N20,000 da bulala 20 a matsayin izina ga sauran al’umma.

A watan Yunin 2017, an tsare wani mai sukar gwamnan, Zakari Kafin Hausa, na tsawon kwanaki saboda sukar gwamnan a dandalin sada zumunta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here