Zargin N240m: Kotu ta Bayar da Umarnin Kama Kwamishinan Ganduje

 

Kano – Babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin kama tsohon Kwamishinan Shari’a a gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kan wasu zarge-zarge da ake yi masa.

Kotun ta bukaci cafke Barista M. A. Lawal, bayan ya gaza bayyana a kotu kan tuhume-tuhume da ake masa da suka hada da batar da makudan kudi har N240m.

Tsohon shugaban hukumar KSIP ya shiga matsala

Leadership Hausa ta ce ana tuhumar Lawal da laifuffuka huɗu masu alaƙa da ɓatar da kuɗi da cin amana da suka kai N240m.

A wata shari’a daban, kotun ta bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon shugaban hukumar na Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP).

An ba da umurnin ne bisa zargin ɓatar da makudan kudi har N212m da ake tuhumar tsohon shugaban kamfanin da karkatarwa a lokacin da yake jan ragamar shugabancinsu.

An ɗage shari’ar ta su zuwa 29 ga Afrilun 2025, bayan abokin shari’arsa, Dauda Sheshe, bai karɓi sammaci ba.

An aike da sammaci ga kwamishinan Ganduje

Shari’ar tsohon kwamishinan shari’a a Kano ta shafi Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar.

A zaman kotun na Litinin 17 ga watan Maris, 2025 masu gabatar da ƙara sun sanar da kotu cewa har yanzu ba a miƙa wa Ganduje sammaci ba, duk da umarnin da aka bayar a baya.

Kotun ta ce duk da an aike wa tsohon kwamishinan a gwamnatin Abdullahi Ganduje sammaci, bai bayyana a gare ta ba wanda hakan ya tilasta fitar da wannan umarni.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa 6 ga Mayun 2025 da muke ciki, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here