Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kammala Sauraron Shari’ar Zaɓen Gwamna Abdullahi Sule
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kammala sauraron shari’ar zaɓen gwamnan jihar Nasarawa.
Gwamnan jihar Abdullahi Sule na jam’iyyar APC ne ya shigar da ƙarar, yana ƙalubalantar hukuncin kotun ƙorafin zaɓe da ta soke nasarar da ya samu a watan Fabrairu, inda ta ayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Kotun mai alƙali uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Uchechukwu Onyemenam, ta shaida wa ɓangarorin da abin ya shafa cewa za ta sanar da su ranar da za ta yanke hukunci.
Read Also:
A zaman kotun na yau Laraba, lauyan Gwamna Sule, Wole Olanipekun, wanda ya shigar da hujjoji biyar don ƙalubalantar hukuncin kotun zaɓen gwamnan Nasarawa, ya buƙaci kotun daukaka ƙarar ta yi watsi da hukuncin ƙaramar kotu.
Olanipekun ya ƙara da cewa kotun ta ƙi amincewa da hujjojin shaidunsu a yayin zaman da ta yi, kuma ba ta yi amfani da bayanai daga na’urar tantance masu zaɓe (BVAS) da aka gabatar mata ba.
Sai dai, lauyan Ombugadu da PDP, Kanu Agabi, ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar da Gwamna Abdullahi Sule ya ɗaukaka.
Agabi wanda ya miƙa wa kotun hukuncin da ƙaramar kotun ta yanke, ya ce a lokacin yanke hukuncin, ƙaramar kotun ta yi cikakken bayani kan yadda ta kai ga yanke hukuncin nata.