Kotu ta Bukaci a Kawo Mata Dan Abdulrasheed Maina

Kotu ta umarci a damko dan Abdulrasheed Maina, Faisal, don a yanke masa hukunci maimakon mahaifinsa.

Hakan ya faru bayan lauyan EFCC, Abubakar Mohammed, ya nemi a kama Faisal a maimakon mahaifinsa.

Ya janyo hankalin alkalin, da cewa Maina da lauyansa sun dade basa bayyana a gaban kotu.

A ranar Talata, babbar kotun tarayya ta Abuja, ta umarci a kama yaron tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, Faisal, bayan kin bayyanarsa a kotu don a cigaba da shari’a a kan zargin ha’inci da ake masa.

Alkali mai shari’a, Okon Abang, ya umarci jami’an tsaro da su kama Faisal duk inda suka gan shi. Kotun ta gayyaci wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaura-Namoda, Umar Galadima, don ya bayyana a gabanta ranar Laraba.

Kotun ta umarci ya bayyana don ya bayar da hojojin da za su hana a kulle shi ko kuma ya biya naira miliyan 60 na beli ga gwamnatin tarayya.

Hakan ya yi daidai da sashi na 352 (4) na dokar 2015 ta adalci ga masu laifi, Vanguard ta wallafa. Alkali Abang, ya umarci EFCC da su hukunta dan Maina, a maimakon shi.

Umarnin ya biyo bayan lauyan EFCC, Abubakar Mohammed ya nemi hakan. Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, bayan Maina da Lauyansa ba su kara bayyana a kotu ba.

Sannan Faisal bai kara bayyana a kotu ba tun 24 ga watan Yuni.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here