Kotun Jamhuriyar Benin na Kokarin Mika Sunday Igboho ga Gwamnatin Najeriya
Rahoto ya bayyana cewa, an samu labarin ranar da za a saurari karar yiwuwar mika Sunday Igboho ga gwamnatin Najeriya.
Rahoton ya ce, a yau Alhamis ne kotu zata zauna don yanke hukunci kan makomar Sunday Igboho.
Lauyoyinsa, ana sa ran za su gabata a gaban kotu don bayyana kokensu da suke dashi a kan gwamnati.
Wata kotu a Jamhuriyar Benin ta tsayar da ranar Alhamis, 22 ga watan Yuli, don fara sauraron shari’ar da ake yi wa Sunday Igboho, dan awaren Yarbawa.
Mai magana da yawun Igboho, Olayomi Koiki ne ya bayyana shirin sauraren karar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuli, in ji PM News.
Read Also:
Dan awaren Yarbawan, wanda har yanzu ke hannun Brigade criminelle a Cotonou zai san makomarsa yayin sauraron karar, jaridar The Nation ta kara da cewa.
Hanyar kare Sunday Igboho Koiki a ranar Laraba ya lura cewa sauraren karar zai baiwa lauyoyin Igboho damar gabata a can da kuma kare karar dan gwagwarmayar.
A cewarsa:
“Zan iya tabbatarwa, zai samu damar da za a saurare shi a kotun Jamhuriyar Benin, suna girmama dokokin kasa da kasa. Za zauna yau (Alhamis) da yardar Allah. Za a yi zaman ne da karfe 10 na safe a kotun Jamhuriyar Benin.
“Kotun za ta yanke hukunci kan makomar mika shi kuma za mu samu damar gabatar da kararmu musamman kan halin Igboho.
“Mun san girman abin da gwamnatin Najeriya ke kokarin yi idan suka yi kokarin ganin sun kamo Igboho amma za su gaza, da yardar Allah.
Nufinsu shi ne su kama shi (Igboho), amma Allah ya yi ya kare shi.”