Kotu ta Kakabawa EFCC Takunkumi a Jihohi 10

 

Abuja – Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Olanipekun Olukoyede ya nuna cewa EFCC ta samu koma baya a ayyukanta.

Olanipekun Olukoyede ya ce EFCC ba za ta iya gudanar da bincike a wasu jihohi 10 na Najeriya ba, sakamakon takunkumin da kotu ta saka mata.

Hukumar EFCC ta yi taro da alkalai a Abuja

Shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana hakan ne a babban birnin tarayya Abuja a ranar Litinin kamar yadda Channels TV ta rahoto.

Olukoyede ya yi maganar ne a taron karawa juna sani ga alkalai (EFCC-NJI) karo na shida a dakin taro na cibiyar shari’a ta kasa da ke Abuja.

Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa taken taron “Hada kan masu ruwa da tsaki wajen yaki da cin hanci da rashawa” ya dace da abin da ake son cimmawa.

Kotu ta kakabawa EFCC takunkumi a jihohi

Duk da cewa Olukoyede bai bayyana jihohin da abin ya shafa ba, amma ya koka da yadda ayyukan EFCC ke ci gaba da samun cikas sakamakon takunkumin kotu da ya hana bincike.

A cewarsa, daga cikin kalubalen da ke fuskantar EFCC akwai yadda kotuna ke dage shari’o’in manya-manyan laifuffuka da hana hukumar kama masu laifi da sauransu.

Ya ci gaba da cewa, akwai bukatar kotuna su daina yawan ba wadanda ake zargi takardar umarnin hana EFCC kama su a duk lokacin da ake son bincikarsu.

Yayin da yake amincewa da matsaloli daga banagren hukumar ta EFCC, Olukoyede ya ce hukumar ta dauki wasu matakai na gyara tsarin bincikenta kamar yadda doka ta tanada.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here