Kotu ta Tsige Shugaba da Manyan Jami’an Hukumar Zaben Jihar Kano

 

Kano – Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta tsige shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Malumfashi.

A hukuncin da ta yanke a ranar Talata, kotun ta tsige Farfesa Malumfashi saboda kasancewarsa dan jam’iyyar NNPP a hukumance.

Aminu Tiga da jam’iyyar APC ne suka shigar da karar, kamar yadda rahoton jaridar The Nation ya nuna.

Kotu ta yi hukunci kan karar APC

Wadanda ake karar dai sun hada da babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Dederi da wasu mutum 14.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a S.A Amobede, ya kuma ce Kabir Zakirai, sakataren hukumar ba ma’aikacin gwamnatin jihar Kano ba ne.

Alkalin kotun ya ce Zakirai bai cancanci a nada shi mukamin ba kamar yadda sashi na 14 na dokar hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano ta shekarar 2001 ta tanada.

“An rusa duk abin da wanda ake tuhuma na takwas ke yi a shirye-shiryen zaben kananan hukumomin jihar Kano a shekarar 2024 kuma shirin ba shi da wani tasiri.”

– A cewar kotun.

Kano: An tsige shugabannin KANSIEC

Mai shari’a S.A Amobede ya ci gaba da cewa:

“Da wannan, kotu ta rusa nadin wadanda ake kara na 8 zuwa na 14 ba tare da bata lokaci ba kuma an kore su daga mukamansu na shugaba da jami’an hukumar.

“An hana su gudanar da zaben kananan hukumomi 44 na jihar Kano da aka shirya yi a 2024 har sai an nada wadanda suka cancanta.”

Ya kuma umurci ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tabbatar da cika sharuddan sashe na 197 (1) (b) da 199 (2) da 200 (1) (a) na kundin tsarin mulkin Najeriya.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here