ɗan Atiku Abubakar: Kotu ta Bada Umarin Kama

Wata babbar kotu a Abuja ta bada umarnin kama dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar bisa bijerewa umarnin ta.

Kotun dai ta bada umarnin da ya mika yayan sa uku a hannun mahaifiyarsu Maryam Sherif wanda ta shigar da kara ta nemi da ya bata yayan bayan ya sake ta.

Lauyan mai kara ne ya bukaci kotu da ta bada umarnin kama Abubakar bayan da ya gaza halartar zaman kotun ranar Alhamis duk kuwa da samun takardar sammaci.

Wata babbar kotu, a Kubwa, Abuja, a ranar Alhamis, tayi umarnin gaggauta kama dan gidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, bisa bijerewa wani umarni da kotu tayi ranar 27 ga Oktoban 2020 wanda ke umartar sa da mika yayansa uku ga mahaifiyarsu, Maryam Sherif, saboda tsaro.

Matar dai ita ce ta shigar da karar kan ya bata yayan bayan mijin nata, Abubakar, wanda ya ke amsa sunan kakansa lamar yadda The Punch ta ruwaito.

Alkalin, Bashir Danmaisule ya yanke hukunci ranar 27 ga Oktoba 2020, inda ya yi umarni a mikawa Maryam yaran.

Amma lauyan ta, Nasir Saidu, ya sake shigar da korafi akan cewa Abubakar ya gaza cika umarnin.

Saidu ya roki kotu da ta nemi wanda ake karar da ya bayyana a gaban kotu ya yi bayanin dalilin da yasa bai cika umarnin kotun.

Da Abubakar da lauyansa Abdullahi Hassan, basu halarci zaman kotun ranar Alhamis ba, duk da cewa ya samu takardar sammaci ta hannun hukumar hana fasakwabri (kwastam) inda ya aiki, tun ranar 3 ga Nuwamba 2020.

Da yake dogaro da wannan batu, Saidu ya roki kotun da ta bada umarnin kama wanda ake karar.

Ya tunawa kotun cewa wanda ake karar ya sha bijerewa umarnin kotun na kin zuwa da yaran a kowane zaman kotu lokacin sauraren karar.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Danmaisule ya ce Abubakar bai halarci shari’ar ba duk da samun takardar sammaci.

Da yake yanke hukunci da sashe na 26 na kotunan birnin tarayya Abuja, ya bada umarnin “gaggauta kama wanda ake karar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here