Zaben Gwamna: Kotun Koli ta yi Watsi da Karar Nnaji ta Bai wa Mbah Nasara

 

Jihar Enugu – Kotun koli ta yi watsi da karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta a zaben gwamnan jihar Enugu, Uche Nnaji, suka shigar a gabanta.

APC da Nnaji dai suna kalubalantar nasasar Peter Mbah na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka yi.

Da yake hukunci a ranar Juma’a, 15 ga watan Satumba, kwamitin mutum biyar na babbar kotun ya riki cewa tawagar lauyoyin APC da Nnaji sun shigar da kara mara tushe balle makama.

Hakazalika, kwamitin ya ce masu karar sun kasa gamsar da babbar kotun dalilin da zai sa a saurari karar da suka daukaka wanda bai da inganci.

A hukuncin da kotun ta yanke, Mai shari’a Tijani Abubakar ya ce tun da aka gano bayanin wadanda ke karar ba shi da inganci, rashin ingancin ya kuma shafi karar da wanda aka shigar da karar a kansa.

Ya ci gaba da yin watsi da bayani da karar da masu karar suka daukaka.

Ƙarin bayani na nan tafe…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com