Ribas: Kotu ta yi Watsi da Shugaban Kwamitin Rikon Kwarya na Jam’iyyar APC

Wani bangare na jam’iyyar APC ya yi martani ga hukuncin kotun daukaka kara wanda ta kori shugaban kwamitin rikon kwaryanta a Ribas.

Wani jigo na jam’iyyar, Isaac Ogbula ya yi magana a kan dalilin da yasa suka karba wannan hukuncin da hannu bibbiyu.

Dan siyasan ya zargi wasu mutane da aikin zagon kasa ga ra’ayoyin jam’iyyar a jihar Ribas.

Kotun daukaka kara ta fatattaki Igo Aguma a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC a jihar Ribas.

Wani bangaren APC na jihar wanda ke samun shugabancin Isaac Ogbobula ya kwatanta hukuncin kotun daukaka karan da abun jinjina, The Nation ta ruwaito.

Ogbobula a ranar Talata, 29 ga watan Disamba ya ce, wannan hukuncin ya kawo saiti tare da tsarki a jam”iyyar.

Kamar yadda jigon jam’iyyar yace: “Muna jinjina ga hukuncin kotun daukaka kara a kan ingantaccen hukuncinta na ranar Talata, wanda ta tabbatar da saiti tare da aike muhimmin sako ga kotunan kasa da ita da su kiyaye shiga lamurran cikin gida na jam’iyyun siyasa.”

Ogbobula ya ce hukuncin kotun ya bai wa jam’iyyar damar cigaba.

Ya yi kira ga jajirtattun mambobin jam’iyyar APC da su ceto jam’iyyar daga hannun ‘yan siyasa ‘yan gangan.

Kamar yadda yace: “Dole ne mu tuhumi tsare-tsare, shirye-shirye da kuma duk ayyukan jihar nan da kuma yadda abubuwa ke kasancewa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here