Kotu ta Yanke wa Jarumar Shirin Fina-Finai a ƙasar Ghana Hukuncin Zaman Gidan Gyaran Hali na Watanni Uku
Wata Kotu daka zaman ta a Accra, babban birnin ƙasar Ghana ya yanke ma wata jarumar shirin wasan kwaikwayo hukuncin zaman gidan gyaran hali na watanni uku.
An yanke ma jarumar hukuncin ne bayan ta aikata laifin bayyana hoton tsiraici a shafinta na kafar sada zumunta.
Jarumar wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta amsa laifinta bayan ta bayyana a gaban kotu An yanke wa Fitacciyar jarumar shirya fina-finai a ƙasar Ghana, Rosemond Alade Brown, wacce akafi sani da Akuapem Poloo, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni uku bisa nuna tsiraici da tayi a wani hoto da ta saka a kafar sada zumunta.
Read Also:
A ranar Jumu’a, wata kotu dake zamanta a Accra, babban birnin ƙasar ta bayyana cewa jarumar zata yi zaman gidan yarinta ne a keɓance kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
Kotun ta kara da cewa wannan hukuncin zai zama izini ga wasu dake da niyyar aikata makamancin abinda Poloo ta aikata. Poloo dai ta turo hotunan ne a kafafen sada zumunta a watan Yuni, 2020, don taya ɗanta murnanar cika shekaru bakwai da haihuwa.
Mutane da yawa ba suji daɗin abinda jarumar ta yi ba, yayinda daraktan kare hakkin ƙananan yara na ƙasar ta Gwana, Bright Appiah, ya shigar da ƙara kotu yana roƙon a hukunta ta.
Akuapem Poloo ta roƙi gafara a kan abinda ta yi, inda ta bayyana cewa ba’a fahince ta bane, ta ɗauki hoton ne don ta nuna ma mutane su rinƙa yab ma mahaifiyarsu.
Sai dai, irin wannan ya saɓa ma dokar yan sandan ƙasar, dalilin hakan yasa aka kama jarumar shirin fim din.
Da farko dai jarumar ta musant zargin da ake mata, amma daga bisani ranar Larabar data gabata ta amince da laifinta a lokacin data bayyana a gaban kotu.