Kaduna: Kotu ta Yanke Hukuncin Wanda Zai Zama Sarkin Zazzau
Babbar kotun jihar Kaduna dake zaune a Dogarawa, Sabon Garin Zariya yanzu nan ta yanke hukumar cewa Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli ne sahihin Sarkin Zazzau na 19.
Read Also:
Daily Trust ta ce Alkali Kabir Dabo, wanda ya yanke hukuncin ya ce gwamnan jihar, Nasir El-Rufa’i zai iya nada sarkin ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, 2020.
Wannan hukunci ya biyo bayan karar da Iyaz Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, ya shigar kan zaben sabon sarkin.