Tijani Umar: N1.3bn ya Yiwa Asibitin Fadar Shugaban Kasa Kadan

Sanatoci sun bukaci ma’aikatan asibiti fadar shugaban kasa su daina bari Buhari na fita kasar waje jinya.

Sanata Danjuma Laah ya ce bai kamata a rika yawo da shugaban kasa idan yana rashin lafiya ba.

Sakataren fadar shugaban kasan ya ce yana bukatan kudi fiye da wanda ake shirin bashi Sakataren din-din-din fadar shugaban kasa, Tjjani Umar, ya ce kudi bilyan 1.3 da aka tanadarwa asibitin fadar shugaban kasa a kasafin 2021 ya yi kadan.

Ya bayyana hakan a hirarsa da manema labarai ranar Alhamis bayan kare kasafin kudin 2021 da ma’aikatarsa ta gabatar gaban kwamitin harkokin gwamnati, Punch ta ruwaito.

Umar wanda yayi alkawarin tabbatar da cewa shugaban kasa, iyalansa da manyan jami’an gwamnati sun samu isasshen kayan lura da lafiya idan aka amince da kudin.

“Kudi N1.3bn gaskiya ya yi kadan idan ka hada da kudin da muka bukata, kudi, ” yace. “Idan aka kwatanta da asibitocin duniya, za ku ga cewa wannan kudi bai yi kusa ko kadan da abinda muke bukata ba.” “Mun dauki wannan asibitin aiki mai muhimmanci saboda muna son kafa tarihi “.

A ranar Alhamis ne majalisar dattijai ta gargadi ma’aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.

A cewar majalisar, yin hakan zai tabbatar da cewa asibitin fadar shugaban kasa ya koma hayyacinsa a cikin shekarar nan.

Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here