Man United: Pochettino zai maye gurbin Solskjaer ?

Manchester United ta soma tattaunawa da tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino kan wataila ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a matsayin sabon kocin kulob din .

Inji jaridar (Manchester Evening News).

Solskjaer na kan tsini saboda rashin nasara a wasanni biyu a jere kuma watakila a kore shi idan har Everton ta doke United a ranar Asabar in ji jaridar (Star).

Watakila ba za a sallami Solskjaer ba koma ya sakamakon wasa ya kaya a ranar Asabar in ji jaridar (The Athletic).

Manajan Manchester United na samun goyon bayan shugabannin gudanarwa na kulob din kuma suna kallonsa a matsayin wanda zai dade yana jan ragamar kungiyar a Old Trafford. A cewar (Sky Sports).

West Brom na duba yiwuwar nada Lee Bowyer, watau manajan kungiyar Charlton idan har ta kori Slaven Bili. In ji jaridar (Mirror).

Mai kulob din Tottenham Daniel Levy ya yi wa Son Heung-min mai shekaru 28 tayin albashi daidai da na kyaftin dinsu Harry Kane domin dan kwallon na Koriya ta Kudu ya ci gaba da murza leda a can. In ji jaridar (Express).

Manyan kulob kulob a Turai ciki har da Manchester City, Barcelona da Juventus sun soma sa ido kan ‘yan kwallon Borussia Marcus Thuram da kum Alassane Plea. In ji jaridar (Bild).

Watakila Real Madrid ta sayi dan kwallon Faransa Paul Pogba da ke murza leda a Manchester United a kan fam miliyan 54.A cewar (AS).

Arsenal za ta tattauna da dan kwallon Masar, Mohamed Elneny domin duba yiwuwar tsawaita kwangilarsa a Gunners. In ji jaridar (Mail).

Kungiyar Schalke ta Jamus na shirin amincewa dan kwallon Turkiya Ozan Kabak ya koma Liverpool a watan Janairu a kan yarjejeniyar da za a kulla a watan Janairu. In ji jarida (Bild).

Duk da irin kwazon da ya nuna a kasar wasa ta bana, dan kwallon Portugal mai shekaru 23, watau Diogo Jota ba shi ne wanda suka so su saya ba saboda a lokacin kungiyar ta fi muradi a kan Ismaila Sarr. In ji jaridar (Mirror).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here