An Cire ‘Dan Wasan Manchester United,Jadon Sancho Daga Tawagar Ingila

 

An cire dan wasan manchester United Jadon Sancho daga cikin ‘yan wasan da za su bugawa ingila wasan samun gurbin buga gasar cin kofin duniya na 2022 da za a yi a Qatar.

Sancho ba zai buga wasan kasar tasa ba da Andorra da kuma Poland saboda raunin da yaji.

A farkon makon nan ne dan wasan mai shekara 21 ya ji raunin, a ranar Alhamis a wasan da sun doke Hungary.

Yanzu dai zai koma kungiyarsa ta Man United, shi kuma mai horaswa Gareth Southgate zai karasa wasanninsa da mutum 23 a tawagar.

Wata sanarwa da Ingila ta fitar ta ce “Muna sa ran Sancho zai samu sauki ta yadda zai iya buga wasan Manchester united da Newcastle ranar Asabar 11 ga watan Satumba.

Sancho ya buga duka wasa uku da Manchester ta yi a Premeir tun bayan komawarsa kungiyar kan kudi £73m da Borussia Dortmund ta Jamus.

Sau daya kuma kungiyar ta fara wasa da shi, wanda ta yi nasara kan Wolves da 1-01 kafin a tafi hutu.

Tsohon dan wasan Manchester City ya ci wa Ingila kwallo uku a wasa 22 da ya buga mata.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here