Taurarin ‘Yan Wasan Kwallon Kafa a 2021

 

Hukumar UEFA ta fito da jerin taurarin ‘yan wasan kwallon kafa na shekarar nan.

A wannan karo babu sunan Cristiano Ronaldo da Lionel Messi a jerin ‘yan kwallon.

Thomas Tuchel da Pep Guardiola za su gwabza a wajen samun kyautar kocin bana.

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA ta fitar da jerin ‘yan wasan da ake sa rai daga cikin su za a samu gwarzon ‘dan wasan shekarar 2020/21.

A wannan karo, babu sunan ko daya daga cikin taurarin da aka saba gani, ‘dan wasan Juventus, Cristiano Ronaldo da ‘dan wasa Lionel Messi.

UEFA ta ce za ta sanar da wadanda suka yi nasarar lashe kyaututtukan bana a ranar 26 ga watan Agusta, 2021, a garin Istanbul, kasar Turkiyya.

‘Yan wasan shekara (Maza)

A rukunin gwarazan ‘yan kwallon kafa na bana, an fitar da jerin ‘yan wasa uku wadanda daga cikinsu za a fito da wanda zai samu kyautar 2020/21.

Wadannan ‘yan wasa su ne:

Kevin DE BRUYNE (Manchester City FC).

JORGINHO (Chelsea FC).

N’Golo KANTÉ (Chelsea FC).

Wanene zai zama Kocin shekara?

A rukunin masu horas da ‘yan wasa, ‘yan jaridar da suka shiga zabe a wannan karo su fito da sunayen masu horas da ‘yan kwallo uku a nahiyar Turai.

Thomas Tuchel (Chelsea).

Pep Guardiola (Manchester City).

Roberto Mancini (Italiya).

Kamar yadda UEFA ta bayyana a shafinta na yanar gizo a ranar Laraba, 18 ga watan Agusta, 2021, a rukunin kocin ‘yan wasan kwallon kafa mata, an samu:

Lluís CORTÉS (FC Barcelona).

Peter GERHARDSSON (Sweden) Emma HAYES (FC Women)

A wajen bikin da za ayi a Istanbul, za a fadi ‘yar wasar da ta fi kowa kokari a kakar wasan bana.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here