Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sirikar Shugaba Buhari, Zahra Nasiru Bayero

 

Zahra Nasiru Bayero ita ce matashiyar da ta sace zuciyar ‘da namiji daya tilo da Buhari ya mallaka.

Ta kasance ‘ya ta biyu a wajen Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Matashiyar na karantar fannin gine-gine a wata jami’a a kasar Ingila.

A cikin ‘yan sa’o’i kadan daga yanzu, Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari daya tilo, zai angwon ce da Zahra, diyar Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi.

Tuni Kano ta fara cika kuma jami’an tsaro sun mamaye wurare masu mahimmanci a cikin garin.

Anan akwai abubuwan ban sha’awa da yakamata ku sani game da surukar shugaban kasar ”mai shigowa”:

‘Yar Sarkin Bichi

Zarah Ado Bayero ‘ya ce ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero mai shekara 20, wanda shi ne na hudu a ‘ya’yan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Baya ga kasancewarsa Sarki, mahaifinta shi ne kuma shugaban kamfanin 9mobile. Shi ne ɗan fari da aka haifa a gidan masarautar Kano da ake kira Gidan Dabo.

Ya kasance hakimin kananan hukumomin Fagge, Tarauni da Nassarawa kafin gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta nada shi a matsayin sarki mai daraja na daya.

Nasabarta da Sokoto

Yayin da mahaifiyar Zarah, Farida Imam, ta kasance diyar shahararren masanin ilimi na Kano, Mal Abubakar Imam (Imamu Galandanci), tsohon Babban Darakta a Afribank Plc, Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar III, yana auran ‘yar uwar Farida, Daily Trust ta rawaito.

Ilimi

Zarah, ita ce ‘yar sarki ta biyu kuma ta karanci fannin gine -gine a Ingila.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here